Wednesday, January 8
Shadow

Gwamnonin Arewa sun doge akan bakarsu cewa ba zasu yadda Shugaba Tinubu ya aiwatar da dokar canja fasalin Haraji ba

Gamayyar gwamnonin Arewa sun sake nanata matsayarsu akan cewa ba zasu yadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aiwatar da sabuwar dokar canja fasalin Haraji ba.

Gwamnonin sun bayyana cewa, sabuwar dokar harajin zata amfani yankin Kudu ne kawai.

Saidai a hirarsa da manema labarai, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya kan aiwatar da sabuwar dokar.

Jaridar Punchng ta zanta da wasu daga cikin wakilan Gwamnonin Arewa inda suka bayyana mata matsayarsu game da sabon kudirin dokar.

Gwamna Muhammad Yahya na jihar Gombe wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin ta Arewa ya bayyana cewa suna nan a matsayarsu ta kin amincewa da sabuwar dokar canja fasalin Harajin.

Karanta Wannan  HOTUNA: Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya je ziyarar ta'aziyyar ràsųwar mahaifiyar Tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar'adua a Katsina

Gwamnan ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Ismaila Misilli inda yace zasu ci gaba da nuna kin amincewa da sabuwar dokar har sai shugaban kasa ya canja matsayarsa.

Yace shi tun kamin hankalin mutane ya kai kan maganar dokar ya fahimci inda aka dosa kuma ya jawo hankali akai.

Shima gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya tabbatar da matsayarsa inda yace baya magana biyu, ya duba amfani da rashin amfanin wannan sabuwar doka ta haraji kuma yana nan akan bakarsa cewa bai amince da ita ba.

Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Abdulrahman Bundi.

Shima Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa har yanzu yana adawa da wannan sabon kudirin doka.

Karanta Wannan  Atiku ya bukaci majalisa ta ƙara wa’adin mulkin Shugaban ƙasa zuwa shekara 6 sannan a mayar da mulkin Najeriya karba-karba tsakanin Kudu da Arewa

Shima ya bayyana hakanne ta bakin kakakinsa, Peter Ahemba inda yace ba maganar gwamna daya ake ba, ana maganar duka gwamnonin jihohin Arewa ne da ‘yan majalisun tarayya sun ce basu amince da wannan sabon kudirin doka ba dan kuwa abinda aka fahimta shine, Jihar Legas da wasu karin jihohin kudu ne kadai wannan kudirin doka zai amfana.

Yace ya rage ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fito ya fahimtar da Arewa ta yanda wannan sabuwar kudirin doka zata amfanesu.

Shima gwamnan jihar Kano, Abba kabir Yusuf ta bakin kakakinsa, Sanusi DawakinTofa ya bayyana cewa bai amince da wannan kudirin dokar ta canja fasalin karba da raba haraji ba.

Karanta Wannan  A karshe dai bayan shan ruwan Allah wadai, Gwamnatin tarayya na shirin yafewa kananan yaran data kai kotu bosa zargin cin amanar kasa

yace za’a cuci mutanen Arewa ne idan aka aiwatar da wannan doka, yace kamata yayi gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajan kawar da talauci maimakon wannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *