Monday, December 16
Shadow

Gyaran fuska da haske

*Daga ofishin Dr saude likitan mata,

GYARAN FUSKA
#Kurkur
#Yis
#Madara
Ki samu madara cokali daya,kurkur karamin cokali,yis kamar kullin naira 10 sai ki kwaba da ruwa ki shafawa fuskarki da daddare da kuma safe sai ki wanke,yana matukar gyara fuska.Fuskarki zata yi wasai tayi kyau

GYARAN FUSKA
#Madara
#Nescape
#Kurkur
#Lalle
Ki samu madara karamin cokali,nescape karamar leda daya,kurkur cokali karami,lalle shima karamin cokali,sai ki kwaba ki shafawa fuskarki in ya bushe sai ki wanke ki ga yanda fuskarki zata yi kyau da haske gami da sheki.

MAGANIN KURAJEN FUSKA DA WASKANE
#Kurkur
#Zuma
#Kwai
#Aloe vera(ki bareta ruwan ake so)
Ki kwaba duka ki shafa da daddare da safe kuma ki wanke,ki ga yanda fuskarki zata yi kyau gami da sheki tamkar ba a taba samun kuraje da waskane a fuskar ba.

SABULUN GYARAN FATA
#Sabulun salo
#Garin kurkur
#Zuma
#Garin lalle kadan
#Sabulun gana
#Madarar turare
#Madarar gari
#Sabulu mai kamshi
#Garin habbatis Sauda
Ki dakasu gaba daya ko ki goge a greater na hannu,sai ki zuba madara,kurkur,zuma da madarar turare ki kwaba gaba daya,ki cuccura ko ki zuba a roba mai murfi ki dinga wanka dashi ki ga yadda jikinki zaiyi laushi,fatarki tayi kyau da haske,kamshi kuma ya kama jikinki.

Anememu a whatsapp akan wannan lambar kamar haka 0708 589 8135

Daga Shafin Ki gyara Kanki da Kanki.

Gyaran Jiki Ga Mata A Saukake:

Mafi yawan mata na son gyara jikinsu dan birge mai gida ko kuma masoyan su, sai dai kuma akan samu akasi wajen yin amfani da abubuwan Turawa wanda suke da matsololi daban-daban sabanin yin amfani da abubuwan da ake da su na amfanin yau da kullum.

Gyara ko tsafta abu ne mai matukar mahimmanci kuma abu ne me kyau muddin ba za a kauce wa addini ba. Hausawa na cewa “in kana da kyau ka kara da wanka” wannan dalilin ya sa wannan shafi ya yi duba da wasu abubuwan karuwa game da gyaran fata har ma da wasu abubuwan dan karuwar jama’a.

Tsarabar da wannan shafi yake dauke da ita ta hada da abubuwa kamar haka:

Macen da take son fatarta ta goge ta yi kyau za ta yi amfani da:

-Lemon Tsami

-Bawon kwai

-Kur-kur

A hade su waje guda a daka su a runka wanka da shi,fata zata kyau yadda ake bukata.

Baya ga haka akwai hadi na musamman wanda in mace ta yi shi duk tsufanta za ta koma yarinya shakaf.

-Ayaba

-Sabulun Salo

-Man Auduga

-Dudu Osun

-Dettol

-Leman Tsami

Shi ma za a hada su waje guda a runka wanka da shi fata tana tsantsi da laushi.

Bayan haka akwai wani hadin na gyaran fata inda za a samu:

Karanta Wannan  Maganin kyan fuska

-Ganyen Magarya

-Man zaitun

-Man Habbatus sauda

A daka ganyen magaryar a zuba a cikin man zaitun da man habbatus sauda a runka wanka da shi.

Hadi na musamman da yake sa fatar mace ta zamo tana tare da sheki, da laushi, har ma aji jikinta yana wani damshi-damshi sai a samu:

-Ayaba

-Lemon Tsami

-Tatacciyar Madara

-kwai guda daya.

A sami ayaba mai kyau a bare ko a matse da hannu, ko a markada yayi laushi, sai a zuba tacacciyar madarar a fasa kwai kamar guda daya, amma farin za’a zuba, sai a matse lemon tsami a gauraya shi a shafa a jiki ya samu kamar tsayin awa daya, sai ayi wanka da ruwan zafi. Idan ana yi kamar kwana uku za’a sha mamaki.

Gyaran fata na ban mamaki ki samu:

-Man zaitun

-Ridi

A daka ridi, amma sai an gyara shi, an shanya ya bushe sai a daka a zuba cikin man zaitun, idan za’a kwanta arinka shafe fuska dashi
Insha allahu zakiga fuskarki ta koma Fes

Daga shafin kowace cuta da maganinta.

*GYARAN FUSKA DA RUWAN KWAI ( EGG )*

+2348037538596
sirrin magunguna

gyaran fuskar mutum kamar haka:

1- Ruwan kwai nada sinadarin gina jiki, da kuma sinadaran Bitamin.

2- Ruwan kwai na rage tsufar fuska Danyen ƙwai.

3- Danyen kwai na kare fuska daga yawaitan fitar kuraje.

4- Danyen kwai na kara ma fuska haske.

5- Ruwan kai na rage kumburin idanu Yadda ake hada ruwan kwai don samun bukata shine, za’a fara turara fuska da ruwan zafi, sa’annan abi da Rose water a shafe fuskar, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.

Daga nan sai a fasa kwai, a cire kwaiduwar, sai a kada farin ruwan kwan, har sai yayi kumfa, bayan nan sai a shafe fuska da wannan ruwan kwai, sai kuma a daure fuskar da takardar ‘Tissue’ a manna a fuskar, a kara samun takardar a sake mannawa a dukkanin fuskar.

Da zarar fuskar ta bushe a haka, sai wanke fuskar, sa’annan a shafe fuskar da kwaiduwar ita ma, sa’annan a wanke, idan an cigaba da wannan tsari, za’a samu biyan bukata.

Daga shafin Sirrin rike Miji.

YADDA AKE HADA SABULU NA MUSAMMAN DOMIN GYARAN FATA DA GYARAN FUSKA DA KUMA HADIN DILKA.

1) DOMIN KYAWUN FUSKA

A samu:-
1 . Garin zogale
2 . Farar albasa
3 .Sabulun ghana
4 . Sabulun Dettol
5 . Sabulun salo

Yadda za a hada.

Ki samu sabulun ghana dana salo dai dai kai daya sai ki samu dettol shima kamar guda 2 sannan sai ki sami garin zogale cokali 2 sai albasa manya guda 2 duk sai ki hada su a turmi ki kirbe su sannan sai ki juye a roba mai murfi zaki dunga wanke fuskarki da shi yanada kyau sosai yana magance kurajen fuska.

2) HADIN DILKA

1 . Dilka da sukari
2 . Lemon tsami
3 . Man zogale
4 . Turaren Du’aul jannah

Yadda za a hada:-

Zaki zuba duk kayan a cikin ruwa sai ki sa wuta amma kadan har sai ya tafasa yayi kumfa sai ki sauke idan ya huce kirinka dangwala kina shafawa a ko ina a jikinki, ki bari ya bushe, zai fara murmushewa da kansa sai ki karasa murje shi sai kiyi wanka da ruwan dumi, fatarki zatayi kyau

Karanta Wannan  Gyaran Gashi

3) SABULU NA MUSAMMAN
A samu:-
1 . Madarar turari
2 . Lalle da dilka
3 . Ganyen magarya
4 . Kur kur
5 . Dudu osun da Detol
6 . Sabulun ghana

a hadasu wuri daya a daka su a turmi mai kyau su hadi jiki sosai sai ki runga wanka da shi.

Daga Shafin Ashmed Online Training.

GYARAN JIKI

Za mu fara da sinadaran gyaran mama, wannan hadin na farko da zan rubuto yana karawa mace girman nono kuma sam ba ya faduwa. Ko da a ce tana shayarwa ne idan har tana amfani da wannan hadin sai dai mu ce Allah san barka.
Uwargida, ki nemi wadannan kayayyakin:
1). Farar shinkafa
2). Garin Alkama
3). Garin habbatus sauda
4). Garin Ayaba (Plantain).
5). Gyada mai malfa (mai zabo)
6). Aya
7). Madarar gari.
8). Zuma

Za ku bare bayan plantain sai a yanka shi, a shanya ya bushe, sai a daka, a hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sai a hada aya da gyadar a markada a tace ruwan. Bayan nan, sai a dora kan wuta a zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da muka hade a guri daya, sai kuma ku zuba garin madara da zuma, ku dama ya yi kauri sai a rika sha safe da yamma. Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya sosai, ki rika sakawa. Ki yi haka na tsawon sati biyu, da yardar Allah za ki samu biyan bukata. Allah ya tamake mu.

Idan kuma baki da halin siyan duka wadannan kayayyakin da na ambata to kina iya yin kunun alkama ki rika sha sau biyu a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da madara ke nan. Ko kuma ki sami garin hulba, ki tafasa ki rika gasa nonon da shi, sai kuma a shafa man hulban a kan nonon a ga abin mamaki sannan kuma a fasa kwan salwa a shafawa nonon, kuma a fasa guda uku a sha su danye. Insha Allahu za a dace.
Ga kuma gyaran jiki da fuska gaba daya
fata tayi laushi da shezi zaki tanadi ababe
kamar haka:
1. Man Zaitun
2. Lalle
3. Kur-kur
4. Madarar ruwa (peak)

Za ku hade wadannan kayan hadin guri guda sai ku kwaba su ku shafe jikinku da fuskar ku, za ku yi wannan hadin kafin ku shiga wanka idan ya bushe a jikin ku sai ku murje sannan sai ku shiga wanka, wannan hadin ya na sa jiki yayi kyau da sheki insha Allahu.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da ayaba

Za ku iyayin wannan ma wanda ake hada:
1. Kur-kur
2. Dilka
3. Zuma kwai
4. Lemon tsami

Za ku hade su a guri guda ku samu ruwan ku kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ku shafe fuskanku, idan kuma har da jiki kuke so, sai ku shafa harada jiki bayan awa daya sai ku shiga wanka za k ga yadda jikinku zai goge. Das da izinin Allah. Domin wannna hadin shi ake kira Dalleliya.

Ga kuma wani hadin har wayan na gyanan fatan jiki zaku tanadi:
1. Lalle
2. Kwaiduwar kwai 3
3. Manja cokali 3
4. Kur-kur

Sai ku kwaba su guri guda ku shafe jikinku zuwa awa guda, sai ku yi wanka da ruwa
zalla sai ku jika duka da ruwan dumi ku shafe jikin da ita sai ku kuma yin wanka.
Allah ya taimake mu.

Idan kuma gyaran fuska ku ke so sai ku tanadi:
1. Dettol
2. Sabulun Ghana
3. Garin Zogale
4. Farar albasa.

Sai ku hade su guri guda ku kurba su a turin ku mulmula ku rinka wanke fusku za
ku ga yadda fuskarku za ta y i kyau. Wannan kuma hadin yanasa fuska ya yi haske ya yi kyau da annuri ya kuma kore kurajen fuska za’a tanadi abae kamar haka: Bawon kankana sai a runka goge guska da shi yana gyara fuska ya yi sumul.

Ga kuma wani hadin duk na gyaran fatar jiki shi ma wannan hadi ne na musamman
wanda ya ke sa fatar mace ta zamo tana tare da shauki da laushi kai har ma zaki ji
jikin ki yana wani damshi damshi wannan hadi ne da yawanci amare ka wai ake yi
wa shi. Za ku tanadi ababen kamar haka:
1. Ayaba
2. Lemon tsami
3. Tataciyar madara
4. Kwai daya

Za ku sami ayaba mai kyau ku bare k matse da hannuku, ko ku markada a
blenda ya yi laushi, sai ku zuba tataciyar madara ku fasa kwai kamar guda daya
amma farin zaku zuba sai ku matse lemoun tsami ku gauraye shi ku shafa a
jikin ku ya samu kamar tsayin awa daya, sai uk yi wanka da ruwan zafi, idan har
kuka lazinci yin haka kamar kwana uku za ku sha mamaki.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *