MAN KADANYA
Man kade na gyara wa mace jikinta, ta rika sheki kamar kwalba a cikin rana. Ana iya amfani da shi ta hanyoyi da dama, amma ga kadan daga ciki:
Gyaran Jiki:
Idan kina da fata busasshiya ko mai gautsi, man kade zai taimaka miki wajen gyara ta.
Ta hanyar shafa shi a fatarki zai sanya ta zama mai matukar taushi da santsi. Yana kashe kurajen jiki da na fuska, sannan yana gyara fata bayan kunar rana.
A lokaci guda yana magance kaushi da kyesbi da cizon kwari. Idan kafarki na da faso ko tana yawan tsagewa, yin amfani da man kade zai taimaka wajen magance hakan.
Man kitso:
Amfani da man kade yayin da ake yin kitso ko yin shamfo na sanya gashi laushi. Yana kara wa gashi tsawo.
Yana da kyawu ki mayar da shi man kitsonki, domin yana hana gashi karyewa.
Baya ga haka zai mayar miki da gashin kanki kamar roba, ko an dan ja shi, ba zai tsinke ba.
A takaice dai ta hanyar amfani da man kade wajen yin kitso zai iya mayar da gashin kanki abin sha’awa a wajen kawaye da sauransu.
Maganin ciwon kashi:
Man kade na taimakawa wajen gyaran kashi, kamar karaya da targade da kuma ciwon baya.
Don haka idan an bar ki a baya wajen amfani da man kade sai na shaida miki cewa, kin yi babbar asara.