Wednesday, January 15
Shadow

Gyaran jiki bayan gama al’ada

A addinin Musulunci bayan mace ta gama jinin Al’ada dolene ta yi wanka dan tsaftace kanta.

A likitance ma sun bayar da shawarar wanke gaban mace bayan gama al’ada da farin ruwa wanda ba’a hadashi da komai ba.

Ana kuma iya amfani da sabulu wanda bashi da kanshi wajan wanke gaban dan karin tsafta.

A aladance kuma ga yanda bayanin yake:


GYARAN GABA BAYAN GAMA AL’ADA
.
Uwargida yana dakyau aduk lokacin da kika gama al’ada ki gyara gabanki kuma ki kara tsaftaceshi sosai domin inganta lafiyarki data maigidanki tare da karawa kanki kima agurin maigidan naki. domin Hada wannan magani kina bukatar Abubuwa kamar haka:-
.

  1. Sabulun Kuka Ko kuma Ruwan Ganyen Gabaruwa
  2. Tazargade
  3. Zuma
  4. Farin Almiski
  5. Auduga
    .
    Yadda za’ai amfani dasu shine :-
    .
    dafarko uwargida zata tafasa wannan tazargade data tanada sai ta tace ruwan tabarshi ya huce sai ta fara wanke gabanta da sabulun kuka ko ruwan gabaruwa. bayan ta gama andauki dan lokaci sai ta kuma wankewa da wannan ruwan tazargade data tace, sai tadauki auduga ta dangwali zuma ta shafe gabanta. sannan sai ta shafa farin miskinta. indai tai haka zata ga abin mamaki da chanji a tare da ita.
    .
    Allah yasa mudace
Karanta Wannan  Alamomin budewar gaban mace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *