Tuesday, January 28
Shadow

Gyaran Najeriya sai Allah>>Inji Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Allah ne kadai da ya halicci Najeriya zai iya gyarata.

Ya bayyana hakane a wajan wani taron Jam’iyyar APC da ya gudana a jihar Katsina ranar Asabar data gabata inda masoyansa da yawa suka taru.

Wannan kalamai nasa sun jawo suka da Allah wadai musamman daga ‘yan jam’iyyun adawa da kungiyoyin fafutuka.

Misali kakakin Jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson ya bayyana cewa, Jam’iyyar APC yaudarar ‘yan Najeriya ta yi duk da cewa ta san bata san hanyar da zata warware matsalolin Najeriya ba amma ta karbi ragamar aikin.

Ya kara da cewa, wannan magana da tsohon shugaban kasar yayi alamace ta cewa APC ta gaza kuma ba zasu iya magance matsalar Najeriya ba inda suka jawowa kasar koma bayan tattalin arziki, ya kuma ce hakan na nuni da cewa koda gwamnatin Bola Ahmad Tinubu a rude take.

Karanta Wannan  DA DUMI-DUMI: Sheikh Isa Ali Pantami da Sheikh Bello Yabo an hadu ido da ido a Sokoto

Shima Mataimakin Shugaban matasa na Jam’iyyar PDP Timothy Osadolor ya bayyana cewa, wannan magana ta Buhari alamace ta cewa bashi da yakinin Gwamnatin Tinubu zata yi abin arziki ina ya kara da cewa, amma kalaman kamata yayi su zama abin hobbasa ga gwamnatin Tinubu dan ta mike tsaye dan yin ayyukan raya kasa dan kada Najeriya ta kkma kamar Sudan ta kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *