
Dr. Hussain Kano wanda ya jawo cece-kuce bayan daya roki Allah yasa kada ya kai matsayin da sai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a ceceshi kamin ya shiga Aljannah, yayi karin Haske.
Yace akwai ingantaccen Hadisi da yace Ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) akan masu aikata manyan zunubaine.
Yace dalilinsa kenan na fadar haka kuma su baffa Hotoro da suka masa raddi sun san da Hadisin, dan haka yace bai yafe raddin da suka masa ba kuma sai sun gani kamin su Mutu.