Friday, December 5
Shadow

Hajji 2025: Rukunin Farko Na Maniyyatan Jihar Borno Sun Tashi Zuwa Ƙasa Mai Tsarki

Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Dakta Umar Kadafur, tare da shugaban kwamitin aikin Hajji na Jihar Borno, Sanata Kaka Shehu Lawan, SAN, sun gabatar da jawabin bankwana ga rukunin farko na alhazan Jihar Borno da suka tashi zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da Hajjin 2025, jiya, a filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ƙasa da ke birnin Maiduguri.

Cikin jawabin da suka gabatar, Sanata Kaka da Dakta Kadafur da sauran membobin kwamitin sun yi wa maniyyatan fatan sauka lafiya da gudanar da aikin Hajji lafiya cikin nasara. Sun kuma buƙaci maniyyatan da su yi amfani da lokacin wajen gudanar da addu’ar zaman lafiya da ci gaba ga Jihar Borno da Najeriya.

Karanta Wannan  Manyan Ma'aikatan mu ne ke ta tafiya lahira akai-akai babu kakkautawa shiyasa muka ce a yi Azumi ko zamu samu sauki>>Ma'aikatar Noman Najeriya

A cewar Kadafur, wanda shi ne shugaban kwamitin aikin Hajji na Jihar Borno na shekarar 2025 kana kuma Amirul Hajji, ya ba da tabbacin gudanar da dukkan wasu tsare-tsare na aikin Hajji cikin nasara duba da cewa gwamna Zulum ya ba da dukkan wasu abubuwan da ake buƙata da za su taimaka wajen samun nasarar domin ganin Mahajjata sun je lafiya sun yi ibada cikin aminci sun dawo lafiya.

“Gaba ɗaya kuna sane da cewa gwamna ya je garin Marte da Ngala da sauran garuruwa masu fama da matsalar tsaro, domin ƙarfafa jami’an tsaro gami da tallafa wa mutanen da rikice-rikicen ya shafa”. Cewar Sanata Kaka.

Karanta Wannan  Gwamnonin Arewa na taro kan matsalar tsaro a Kaduna

Amirul Hajjin, ya kuma yi kira ga maniyyatan da su kasance masu bin doka da ƙa’ida gami da ɗabbaƙa ɗa’ar da aka san maniyyatan Jihar Borno da ita shekaru aru-aru da suka gabata. Ya kuma ƙara da yi musu addu’ar sauka lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *