Wednesday, January 15
Shadow

Hamas ta soki Blinken kan kalamansa game da batun tsagaita wuta

Hamas ta mayar da martani ga suka daga sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dangane da jan ƙafa wajen amincewa da ƙudurin tsagaita buɗe wuta, inda ta ce ta yi abin da ya kamata game da tattaunawar zaman lafiya.

Hamas ta bayyana cewa ta yi abin da ya kamata dangane da sabuwar shawarar tsagaita buɗe wuta da kuma duk shawarwarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” inda ta banbanta matsayinta da Isra’ila, wanda ta ce ba ta fito fili ta bayyana amincewa da shirin tsagaita buɗe wuta ba.

Blinken ya sha ambata cewa Isra’ila ta amince da shawarar tsagaita wuta, kodayake gwamnatin Isra’ila ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba.

Karanta Wannan  A karshe dai, ba dan yana so ba, Shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da Tsagaita Wuta akan Falas-dinawa bayan Tursasawar kasar Amurka

Da yake magana a Qatar a ranar Laraba, Blinken ya bayyana taƙaicin yadda Hamas ta mayar da martani, yana mai cewa Hamas ta gabatar da sauye-sauyen da ba za su iya yi ba.

Hamas ta yi tambaya kan ko da gaske ne Isra’ila ta amince da shirin, tana mai nuni da cewa firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bai fito fili ya amince da tsagaita bude wuta ba.

Saɓanin haka, Hamas ta jaddada “matsayinta mai kyau kan tsagaita wuta a Gaza” kan jawabin Biden da kudurin Majalisar Dinkin Duniya.

Blinken ya bayyana cewa Netanyahu ya “ƙara jaddada aniyarsa” kan shawarar tsagaita bude wuta a wani taro a ranar Litinin, amma Netanyahu bai amince da shirin a bainar jama’a ba.

Karanta Wannan  Hotunan Sojojin Israela da aka kashe a wajan yaki da falasdinawa

Hamas dai ta dage a rubuta garantin cewa Isra’ila za ta kawo karshen yaƙin kafin ta amince da shirin tsagaita wuta yayin da Netanyahu ya bayyana cewa yaƙin ba zai kare ba har sai an lalata karfin mulki da soja na Hamas tare da kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Yaƙin Isra’ila da Hamas dai ya fara ne a ranar 7 ga Oktoba lokacin da Hamas ta kai wa Isra’ila hari, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,200 tare da yin garkuwa da 251 zuwa.

A cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas, sama da mutum 37,000 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila tun daga lokacin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda dan majalisar kasar Faransa ya daga tutar Falas-dinawa a yayin zaman majalisar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *