Friday, December 5
Shadow

Hankula sun tashi bayan da aka dauke wutar lantarki a kasar Faransa na tsawon awanni 5

Rahotanni daga birnin Riviera na kasar Faransa inda ake bikin fina-finai na kasa da kasa na cewa, an dauke wuta na tsawon akalla awanni 5.

Hakan ya kawo tarnaki a bikin finafinan da ake yi inda baki da dama da suka je wajan bikin ke kokawa musamman game da maganar kudi da zasu yi hidima dasu saboda bankuna da ATM duk sun samu tangarda saboda rashin wutar.

Rahotanni sun ce wasu bata garine suka lalata kadarorin wutar lantarkin wanda hakan ya kawo tarnaki aka dauke wutar.

Lamarin ya zowa mutane da mamaki ganin kasa me ci gaba irin Faransa ta samu matsalar wutar lantarki haka.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamna Fubara da mataimakinsa daga mukaminsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *