
Me magana da yawun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu yace har yanzu akwai kyakkyawar alaka tsakanin Shugaba Buhari da Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a Trust TV yayin wata hira da aka yi dashi.
Malam Shehu yace Buhari yakan ce ba zai zama Butulu ba, Jam’iyyar data bashi damar zama shugaban kasa sau biyu, ba zai mata zagon kasa ba.
Sannan yace duk wanda ya san yanda aka hada APC da gwagwarmayar da aka sha har ta ci zabe, ba zai so yayi wani abu da zai kawowa jam’iyyar tangarda ba.