
Zuwa safiyar yau babu wani karin bayani game da Jirgin sama na sojojin Najeriya C-130 da sojoji 11 da kasar Burkina Faso ta kama.
A daren jiya ne dai Kasar ta Burkuna Faso ya sanar da kama jirgin da sojonin bayan da suka shiga sararin samaniyar kasar ba da izini ba.
Hukumomin kasar dai sun ce suna kan bincikene.
Sannan sun yi gargadin cewa duk wani Sabon Jirgin da ya kara ketawa ta sararin samaniyar su ba da izini ba kakkboshi zasu yi ba wata kakkautawa.