Jami’ar hukumar tsaro ta FBI a Amurka, Alethea Duncan, ta ce ta karɓe ragamar bincike kan harin da wani direba ya kai wa masu bikin sabwar shekara a birnin New Orleans.
Yayin jawabin da ta yi, ta ce “wannan ba harin ta’addanci ba ne”, abin da ya saɓa da kalaman magajin garin.
Zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa aka samu mabambantan bayanai ba game da lamarin da ya jawo mutuwar mutum 10.
Duncan ta ce akwai yiwuwar wani abin fashewa da aka gano a wurin kuma ana binciken gano gaskiyar hakan.
Ta ce mutane za su ƙaurace wa wurin “har sai mun gano abin da ke faruwa”.