Friday, July 12
Shadow

Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 8 a Maiduguri da jikkata wasu da dama

Rahotanni daga jihar Borno na cewa harin Bom ya kashe akalla mutane 8 da jikkata mutane da dama.

Harin wanda na kunar bakin wakene mahara 4 ne suka kaishi kuma rahoto yace dukansu sun mutu.

Hukumar ‘yansandan jihar ta tabbatar da mutane 8 ne suka mutu inda wasu 15 suka jikkata.

Kakakin ‘yansandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya bayyana cewa lamarin ya farune da misalin karfe 3:40 na safiyar yau,Rabar, 29 ga watan Yuni.

Rahoton yace wata mata dake goye da yaro ta tayar da bom din a tashar motar Mararraba dake T. Junction dake garin Gwoza.

Matar da dan da take goye dashi da wasu 6 sun mutu.

Karanta Wannan  Mugunta ko cin Amana? Ji yanda shugaban wani kauye a jihar Katsina ya karbi cin hancin Naira dubu dari bakwai(700,000) ya amince aka kaiwa mutanen kauyensa hari har aka kash-she 30

A bangaren jaridar Premium times kuwa, tace mata 4 ne suka tayar da bamabamai a bangarori daban-daban na jihar wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba’a kai ga tantance yawansu ba ciki hadda soja.

Kafar tace Bom din farko ya tashi ne a tashar mota dake Gwoza inda na biyu ya tashi a wani shingen tsaro na sojoji wanda ya kashe soja daya da farar hula 2.

Na uku ya tashine a wani babban shagon sayayya inda Bom na hudu ya tashi a makabarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *