Akwai hade-haden abubuwa a gida da zasu kara miki hasken fuska sosai ba tare da kin sayi man shafawa mw tsada ba.
Ga abubuwan kamar haka:
Ana hada Lemun tsami, Zuma da Madara:
Ana saka babban cokali na madara sannan a saka karamin cokali na zuma sai a saka babban cokali na ruwan lemun tsami a dama.
Idan suka hadu sosai, sai a shafa a fuska a bari zuwa mintuna 20 a wanke.
A ci gaba da yin hakan zuwa sati 1 ko 2, wannan hadi yana sa fuska ta yi fari sosai.
Ana kuma yin amfani da ruwan dankalin Turawa.
Yanda ake yinshi shine za’a fere dankalin sai a yankashi kanana-kanana a saka a cikin ruwa a rika dauko dankalin aka shafawa a fuska.
Ana kuma iya markada dankalin ko a kirbashi, a matse ruwan jikinshi da rariya ko abin tatar koko.
Ana iya shafawa a fuska a kwanta dashi, da safe a dauraye.
Hakan yana saka fuska ta yi haske sosai matuka.
Hakanan dan samun hasken fata cikin kankanin lokaci, ana iya samun shinkafa rabin kofi a nikata a tankade a samu garinta me laushi sosai a hada da madara cokali 3-4 a kwaba a shafa a fuska.
Hakan na matukar sanya fuska da yi haske sosai idan aka ci gaba da yi akai-akai.
[…] Lafiyar Fata: Lemon tsami yana taimakawa wajen gyara fata, rage kuraje, da kuma kara hasken fata saboda sinadarin vitamin C da ke […]