Sunday, March 16
Shadow

Hattara: An gano masu gasa kaji na gefen hanya suna amfani da lalatatun Kaji

Wani Rahoto na musamman da Jaridar Vanguard ta yi ya gano cewa wasu masu gasa kaji na gefen hanya na amfani da kajin da suka lalace suna sayarwa mutane.

Rahoton yace matsin tattalin arziki da rashin kasuwa yasa dole wasu masu gasa kajin da nama na bakin titi suka daina kasuwancin.

Inda wasu kuma a kokarin rage Asara da ci gaba da kasuwancin kamar yanda hausawa ke cewa da babu gara ba dadi ke siyo kajin da suka dade a ajiye suka fara lalacewa.

Rahoton yace masu sayarwa da masu gasa kajin naman sukan ajiyesu a firjin ne, to dalilin rashin kasuwa, idan kajin suka dade ba’a siya ba sai su fara lalacewa har dandanonsu ya fara canjawa.

Karanta Wannan  Muna kokarin ganin kowane gida ya wadata da abinci>>Shugaba Tinubu

Amma maimakon a yaddasu, saboda gudun Asara, sai a rika sayarwa da masu gasa naman irin wadannan kaji da suka fara lalacewa a farashi me sauki.

Su kuma sukan yi amfani da magi da sauran dabaru nasu na masu gashi dan su rufe wannan canjin dandano na kajin.

Jaridar ta Vanguard ta yi hira da wasu da suka sayi irin wadannan kaji da basu ji dadin hakan ba.

An dai yi kira ga hukumomi da su saka ido akan irin masu wannan ha’inci musamman dan kare lafiyar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *