Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta tabbatar da kama wani ɗan kasar China bisa zargin taimaka wa ƴan ta’adda.

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta tabbatar da kama wani ɗan ƙasar China yayin wani samamen yaƙi da ta’addanci da aka gudanar a Jihar Borno.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo- Markus Kangye, ne ya tabbatar da hakan a madaJanardin manyan hafsoshin soji a ranar Juma’a.
Sai dai Manjo-Janar Kangye bai bayyana sunan baƙon ba, amma ya ce mutumin da ya bayyana kansa a matsayin mai hakar ma’adanai yana hannun dakarun soji yanzu kuma ana ci gaba da bincikarsa.
Kama ɗan ƙasar China ɗin ya faru ne kasa da mako guda bayan rundunar soji ta bayyana kama wasu ‘yan Pakistan huɗu da ake zargin suna koyar da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
Yayin da ake tambayarsa game da kasancewar mutumin a yankin da ake gudanar da ayyukan soji, Janar Kangye ya ƙara da cewa an kama wasu mutane biyar da ke bai wa ‘yan ta’adda kayayyakin more rayuwa a lokacin samamen.
Kakakin tsaron ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin manufar mutumin da kuma yiwuwar dangantakarsa da kungiyoyin ta’addanci.