‘Yansanda a jihar Anambra bisa hadin gwiwar kungiyar ‘yanci sun kama wani magidanci me shekaru 46 bisa zargin yiwa diyarsa me shekara daya fyade.
Mutumin me suna Christopher Ugwunna Azubuike An kamashi ne a kauyen, Uratta Amaogwugwu dake karamar hukumar Isialangwa North a jihar.
Diyar tashi ita daya ce tilo suka haifa wadda ke da shekara 1 da watanni 9 da haihuwa bayan sun shafe shekaru 5 da yin aure.
An kai yarinyar Asibiti kuma likitoci sun tabbatar da cewa an mata fyade.
Wanda ake zargin yana hannun ‘Yansanda kuma ana ci gaba da bincike.