An kama matar aure, Barkisu Sulaiman a garin Karaworo,Lokoja jihar Kogi bayan data jefar da dan data haifa a kwata.
Matar dai mijinta bashi da lafiya yana kwance yana jinya.
Shine aka samu wani daga cikin yaran mijin ya rika lalata da ita har ciki ya shiga.
Anan ne dai yaron mijin ya tsere sannan kuma yace bashi ne ya mata cikin ba kuma ta gaggauta zubar da cikin.
Tuni dai jama’ar gari suka kamata suka mikata wajan hukumar NSCDC. Jami’in hukumar na jihar Kogi, Paul Igweibuke ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna tsare da matar.
Mijin Barkisu dai ya samu matsalar ciwon laka watau Spinal Code wanda hakan ne yasa baya iya tabuka komai.
Ita kuma bayan da yaron mijin ya mata ciki sai ta jefoshi daga saman bene cikin kwata.