Wednesday, January 15
Shadow

Hoto: ‘Yan Sanda Sun Cafke Masu Karbar Adai-daita Sahu Na Sata

Jami’an ‘yan sanda a jihar Adamawa sun kama wasu matasa biyu da ake zargi da karbar babur mai uku na sata.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta samu ranar Alhamis, inda ta ce ta kuma kwato babur din da aka sace.

“A ranar 28 ga watan Mayu, 2024, rundunar ‘yan sandan Adamawa ta samu bayanai game da wani keken napep da aka sace a kan titin Chochi, Rumde, Yola ta Arewa” in ji rundunar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai daukar hotonta na SP Suleiman Nguroje.

“Bayan samun labarin, an tura tawagar ‘yan sanda masu sanya ido a hedikwatar Jimeta Divisional ba tare da bata lokaci ba. An yi sa’a, an kama wani Yusuf Adamu mai shekara 18 da kuma Abdul Salam Abubakar mai shekaru 18 a lokacin da suke kokarin sayar da babur din,” in ji ‘yan sandan.

Karanta Wannan  Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, babur din mai kafa uku an sace shi wanda har yanzu ba a kama wanda ake zargi ba kuma wadanda ake zargin suka karba.

Nguroje ya ce, “An gano wani Mohammed Sani a matsayin mamallakin babur din mai kafa ukun da aka sace,” in ji Nguroje, ya kuma kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Dankombo Morris, ya yaba da bayanan da jama’a suka bayar a kan lokaci da suka taimaka wajen kama wadanda ake zargin tare da dawo da Adai-daita Sahun.

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *