Sunday, December 14
Shadow

Hotuna: EFCC Ta Kama Masu Zamba a Yanar Gizo 120, Ta Kwato Motoci Masu Tsada a Jihar Legas

EFCC Ta Kama Masu Zamba a Yanar Gizo 120, Ta Kwato Motoci Masu Tsada a Jihar Legas.

A ranar Litinin ɗinnan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta (EFCC) reshen Lagos ta kama mutane 120 da ake zargi da aikata zamba ta yanar gizo — maza 95 da mata 25 — a wani samame da aka kai a wurare daban-daban cikin jihar Legas.

An gudanar da samamen ne bayan samun sahihin bayanan sirri kan ayyukan masu damfara ta intanet.

Abubuwan da EFCC ta kwato sun hada da:

Motoci masu kyau guda 26

Kayan adon alfarma

Wayoyi masu kyau da kwamfutoci

Takardu da shaidu da ke da nasaba da zamba ta intanet

Karanta Wannan  Duka kwalejojin ilimi a Najeriya za su fara ba da shaidar digiri

EFCC ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike a kan wadanda ake zargin, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala binciken.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *