Friday, July 17
Shadow

Hotuna: Gawar marigayi shugaban sojojin Najeriya, Lagbaja ta isa Legas

Rahotanni daga Legas na cewa, gawar marigayi shugaban sojoji, Lt. Gen. Taoreed Lagbaja ta isa Jihar inda za’a yi jana’izarsa.

Gawar ta sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas din da safiyar ranar Alhamis.

A ranar Larabar data gabata ne dai gwamnatin tarayya ta tabbatar da mutuwar shugaban sojojin.

Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da cewa ranar November 15, 2024 za’a yi jana’izar marigayin a makabartar sojoji dake Abuja

Karanta Wannan  Sabuwar Baraka ta kunno kai a jam'iyyar ADC, Ana zargin Atiku da saye duk wani me fada aji a jam'iyyar da kudi, Peter Obi ya koka da cewa an mayar dashi saniyar ware

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *