Hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi NDLEA ta kama wani dan fim din Najeriya me suna Emeka Emmanuel Mbadiwe da miyagun kwayoyi.
An kamashi ne ranar Juma’a, 27 ga watan Disamba na shekarar 2024.
An kama Emeka ne bayan da ya aika yaronshi ya je filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas dan karbomai kwayar da aka aiko masa daga kasar Amurka.
Tuni dai aka tasa keyarsa dan ci gaba da bincike.