Jirgin kasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna yayi hadari a yau, Lahadi.
Jirgin yayi hadarin ne a daidai Jere.
Jirgin ya tashi ne daga Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe 8:05 na safiyar ranar Lahadi.
Kuma ya sauka daga kan titinsa a daidai garin Jere.
Jami’an tsaron sojoji dana ‘yansanda sun je wajan da hadarin ya faru.
Hukumar NIBS ta sanar da cewa tana sane da faruwar lamarin kuma ta tura jami’anta zuwa wajan.