Matashi Khalid Aminu kenan a wadannan hotunan bayan da wanda suka nuna yanda yake kamin a kamashi da kuma yanda ya koma bayan an sakoshi daga hannun hukumar tsaro ta kasa, DSS.
An kamashi ne dai bayan da ya shiga yin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a baya kuma ya shafe makonni 11 a tsare inda gwamnati ta tuhumeshi da tunzura jama’a a kotu, saidai yayi nasara akan gwamnatin.
Ya wallafa bayanai a shafinsa na sada zumunta inda yake kara tabbatar da cewa gwiwarsa ba ta yi sanyi ba da yin fafutuka.
Ya kuma godewa duka wanda suka nuna masa goyon baya a yayin da aka kamashi ciki hadda mahaifinsa da mawallafin jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowore.
Shima dai Sowore wanda kuma tsohon dan takarar shugaban kasa ne ya bayyana jinjina ga Khalid.
Zanga-zangar tsadar rayuwa dai na daga cikin manyan abubuwan da suka faru a Najeriya cikin shekarar nan da muke ciki wadda ta bayyana irin fushin da jama’a ke ciki game da yanayin mulkin su da ake.