Rahotanni daga jihar Naija na cewa masu kwacen waya sun kashe wani matashi me suna Muhammad Abdulmutalib a babban birnin jihar Minna.
Lamarin ya farune da misalin karfe 8 na yammacin ranar Lahadi October 6, 2024 a 123 quarters, Old Secretariat Road yayin da yake kan hanyar zuwa gida.
An garzaya dashi asibiti amma acan rai yayi halinsa.