Me wasan Barkwanci a Najeriya, Zicsaloma ya je kasar Turkiyya inda likitoci suka mikar masa da hancinsa.
Zicsaloma ya hau shafinsa na sada zumuntar Instagram inda ya bayyana hakan.
Kuma ya bayyana cewa,mikar da hancinsa abune da ya dade yana ta kokarin yi.
Ya bayyana cewa, likitocin sun gaya masa sai an tada wasu komada a fuskarsa kamin a samu damar yi masa gyaran fuskar kuma tuni ya amince da hakan.