Friday, February 7
Shadow

An kama me gàrkùwà da mutane bayan da ya kai ziyarar jaje ga wanda ya sace har gida

Mahukunta a garin Kwantagora dake jihar Naija sun kama wani me garkuwa da mutane.

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da kamen a karshen makon da ya gabata, yace wanda ake zargin, Nasiru Isyaka na tare da wasu gungun masu garkuwa da mutanene da suka kai hari kauyen Sabon-Gari Mangu Matachibu inda suka kashe mutum daya da yin garkuwa da wasu biyu.

Nasiru Isyaka dai shima dan garin Sabon-Gari Mangu Matachibu kuma bayan da aka kubutar da wadanda suka yi garkuwa dasu, ya je yi masa jaje inda a nan ne ya ganeshi.

Ya kara da cewa an kwace bindiga hadin gida guda daya daga hannunsa sannan kuma ya amsa laifin da ake zarginsa dashi.

Karanta Wannan  Hotuna:Rahama Sadau tawa masoyanta gaisuwar barka da sabon wata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *