Wednesday, January 15
Shadow

Hotuna: NLC ta kulle Asibitin Kano

Marasa Lafiya na fama da kansu inda suka rasa madafa a asibitin Muhammadu Abudullahi Wase Teaching dake Kano saboda yanda ma’aikatan Asibitin suka ahiga yajin aikin NLC.

Jaridar Daily Trust tace marasa lafiya da yawa da suka je ganin likita asibitin sun yi cirko-cirko saboda rashin likitoci.

Wasu dole haka suka koma gida ba tare da sanin ranar da zasu sake komawa ganin likitan ba.

Wata mata me fama da ciwon suga Binta Muhammad ta bayyana cewa, da tasan ba zata samu ganin likita ba da bata fito daga gida da wuri haka ba.

Saidai wata majiya daga asibitin tace har yanzu ana kula da marasa lafiya wanda suke da matukar bukata.

Karanta Wannan  Gwamnatin Najeriya ta roƙi 'yan ƙwadago su janye yajin aiki

Bayan asibitin, Majalisar Jihar Kano, ofishin shugaban ma’aikata, babbar kotun jihar Kano, da kotun daukaka kara da sauran manyan ma’aikatu duk a kulle suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *