Wata budurwa data zauna akan cinyar mahaifinta ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.
An ga budurwar da shigar banza inda ta zauna akan cinyar mahaifinta tana masa murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Saidai da yawa sun yi Allah wadai da abinda ta aikata inda suka ce bai dace ba.
Da yawa dai sun bayyana abinda budurwar ta aikata a matsayin rashin da’a.