Hukumar dake shirya gasar Euro wato (UEFA), ta bayyana wasu sabbabin dokoki guda uku da za a fara amfani da su a gasar ta bana wadda zata gudana a ƙasar Germany.
- Alƙalin wasa zai bayyana hukuncin da ya yanke kuma zaiyi bayanin hakan ga magoya baya ta hanyar sadarwar kunne kai tsaye (Headphones)
- Za a dinga bayar da bayanai kai tsaye zuwa ga masu sharhin wasa (Commentators) akan hukuncin alƙalin wasa bayan dawowar sa cikin fili daga ganin VAR domin a yiwa masu bibiyar wasan bayanin abun da ya faru kai tsaye.
- A kowacce ƙwallo za a saka na’ura wadda zata dinga fayyace wa alƙalin wasa satar gida da kuma batun taɓa ƙwallo da hannu a yadi na 18.
- Fagen Wasanni