
Hukumar DSS ta kama wani mutum me suna Innocent Chukwuma saboda kiran da yake yiwa sojoji su yi juyin Mulki wa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Hukumar ta kamashi ne a Oyigbo dake Fatakwal jihar Rivers.
Hukumar ta yi ta bibiyarsa inda ta lura yana yawan kira ga sojoji da su yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki bosa zargin rashin Adalci.