Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC na fama da matsalar jami’anta da ake kamawa da satar kudade da kadarori da aka kwato daga hannun jami’an gwamnati da masu rashawa da cin hanci.
Wasu daga cikin jami’an hukumar an koresu daga aiki inda wasu kuma aka dakatar dasu dan yin bincike kan zargin satar kayan da aka basu kula wa dasu.
Koda a shekarar data gabata, mutane 27 ne aka kora daga EFCC saboda satar kudaden da aka basu ajiya
Hakanan kakakin EFCC a ranar 6 ga watan Janairu 2025 ya tabbatar da cewa suna binciken batan dala $400,000 da ake zargin wani jami’in hukumar ya sace.
Hakanan akwai jami’an hukumar 10 da aka dakatar a reshenta na jihar Lagos inda ake zarginsu da satar Gwal da darajarsa ya kai na Naira Biliyan 1, da kudade dala $350,000 zuwa $400,00 wanda duka suka bace a hannunsu.
Hakanan a ofishin hukumar EFCC na jihar Kaduna ma wasu dala $30,000 sun sake bacewa, sadai hukumar ta EFCC ta shiru akan lamarin bacewar kudin.
Wani ma’aikacin hukumar ta EFCC da jaridar Punchng ta zanta dashi yace tsadar rayuwa da karancin saun kudi ne yake jefa ma’aikatan nasu cikin irin wannan hal8