Friday, December 5
Shadow

Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya ta kara yawan ziga-zirgar jirgin saboda tafiye-tafiyen Sallah

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, (NRC) ta kara yawan zirgazirgan jirgin kasar dake Jigila daga Legas zuwa Ibadan.

Hakan na zuwa ne yayin da mutane ke ta tafiye-tafiye dan shagulgulan Sallah.

Me magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu ne ya bayyana haka inda yace jirgin dake Jigila tsakanin Warri-Itakpe shima zai yi aiki na musamman a ranar Alhamis.

Sannan yace jirgin Kaduna zuwa Abuja an kara mai yawan tarago.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Kananan yaran da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu bisa zargin cin amanar kasa na iya fuskantar hukuncin kìsà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *