
Hukumar sararin samaniya ta Najeriya, (NiMet) ta yi hasashen samun Gajimare da rana a wasu sassan Najeriya daga ranar Laraba har zuwa Juma’a.
A sanarwar data fitar ranar Talata a Abuja, Hukumar tace za’a samu rana a jihohin Arewa daga ranar Laraba zuwa Juma’a.
Tace amma za’a iya samun hadari a sararin samaniyar jihohin Kaduna, Adamawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Taraba da kuma tsawa.
Hakanan tace a jihohin Benue, Plateau, Niger, Kwara da Kogi ma abinda ake tsammanin zai faru kenan.
A jihohin Delta, Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Bayelsa kuma sun ce za’a samu hasken rana da safe inda suma ana tsammanin Hadari da tsawa.
A jihohin Kebbi, Taraba, Borno da Adamawa kuwa hukumar tace za’a tashi ranar Alhamisbda tsawa.