Sunday, November 16
Shadow

Hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya ta yi hasashen samun Gajimare da tsawa a fadin kasar

Hukumar sararin samaniya ta Najeriya, (NiMet) ta yi hasashen samun Gajimare da rana a wasu sassan Najeriya daga ranar Laraba har zuwa Juma’a.

A sanarwar data fitar ranar Talata a Abuja, Hukumar tace za’a samu rana a jihohin Arewa daga ranar Laraba zuwa Juma’a.

Tace amma za’a iya samun hadari a sararin samaniyar jihohin Kaduna, Adamawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Taraba da kuma tsawa.

Hakanan tace a jihohin Benue, Plateau, Niger, Kwara da Kogi ma abinda ake tsammanin zai faru kenan.

A jihohin Delta, Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Bayelsa kuma sun ce za’a samu hasken rana da safe inda suma ana tsammanin Hadari da tsawa.

A jihohin Kebbi, Taraba, Borno da Adamawa kuwa hukumar tace za’a tashi ranar Alhamisbda tsawa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda hukumar Babban birnin tarayya Abuja ta kulle babbar sakatariyar PDP dake birnin saboda rashin biyan Haraji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *