Monday, May 26
Shadow

Hukumar raba arziƙin ƙasa ta nemi sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi a Najeriya

Hukumar rarraba arziƙin ƙasa (RMAFC) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi 774 da yadda ake aiwatar da sabuwar dokar man fetur (PIA).

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban hukumar, Dr. Muhammed Shehu, da Sakatarenta, Injiniya Joseph Okechukwu Nwazeb.

hukumar ta fitar da sanarwar ne bayan taron horarwar kwana uku da aka gudanar a Uyo, Jihar Akwa Ibom inda taron ya mayar da hankali kan inganta tsarin kuɗi da rarraba albarkatu a Najeriya.

Sanarwar ta ce “Ya zama dole a riƙa biyan kuɗaɗen kananan hukumomi kai tsaye daga asusun tarayya ba tare da tsoma bakin gwamnatocin jihohi ba.”

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda wata mata ta guntulewa wata yatsa da cizo saboda Namiji

Haka kuma, hukumar ta buƙaci a sauya Sashe na 162(2) na kundin tsarin mulki domin sanya lokaci na musamman da shugaban ƙasa zai gabatar da tsarin rarraba kuɗaɗen shiga na RMAFC ga majalisar ƙasa.

Wannan, a cewarsu, zai taimaka wajen ganin an raba albarkatu cikin lokaci da adalci.

Dangane da Dokar Man Fetur kuwa, RMAFC ta ba da shawarar a faɗaɗa kwamitin gudanarwa na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) domin haɗa wakilai daga jihohi da ƙananan hukumomi, da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *