Friday, May 9
Shadow

‎Hukumar tace fina-finai ta Kano ta fara kamen Baburan Adai-daitasahu masu ɗauke da hotuna da rubuce-rubuce na rashin ɗa’a




‎Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta kaddamar da wani sabon atisayen kama baburan adai-daita sahu da ke dauke da hotunan batsa da rubuce-rubuce marasa tarbiyya a manyan titunan jihar.

‎Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ne ya tura jami’an sa don gudanar da wannan aiki, inda ya bayyana cewa hakan na daga cikin nauyin da ke kan hukumar na tabbatar da tsaftar hotuna da rubuce-rubuce da ke bayyana a fili ga al’umma.

‎Sanarwar ta fito ne daga Abdullahi Sani Sulaiman, Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano.


‎“Aikinmu shi ne tabbatar da cewa babu wani hoto ko rubutu da zai cutar da tarbiyya ko dabi’un al’umma, musamman matasa, ya fito fili ba tare da tantancewa ba,” in ji Abba El-Mustapha.


‎Daraktan Sashen Dab’i na hukumar, Alhaji Abubakar Zakari Garun Babba, ya bayyana damuwa kan yadda wasu matukan babura ke lika hotuna da kalmomi da ke sabawa tarbiyyar al’umma a jikin baburansu. Ya ce wannan lamari ba za a lamunta da shi ba, kuma hukumar za ta ci gaba da gudanar da wannan aiki a fadin jihar.


‎A karshe, ya bukaci matukan babura da su guji aikata irin wadannan laifuka da ka iya janyo musu fushin doka, tare da yin kira ga al’umma da su bada hadin kai da goyon baya ga hukumar domin ci gaban jihar.

Karanta Wannan  Najeriya ce kasa ta daya a Afrika sannan ta 2 a Duniya wajan yawan yaran da basu samun abinci me gina jiki>>Inji UNICEF

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *