Sunday, March 16
Shadow

Hukumar ‘yansandan Abuja ta ce tsohon shugaban hukumar Immigration David Shikfu Parradangba garkuwa aka yi dashi ba, ya mutu ne a dakin Otal bayan sun shiga shi da wata mata

A dazu ne dai muka samu rahoto daga jaridar The National cewa tsohon shugaban hukumar shigi da fici, Immigration me suna David Shikfu Parradang an yi garkuwa dashi kuma an kasheshi.

Saidai sabbin bayanai da hukumar ‘yansandan Abuja suka fitar sun ce ba a yi garkuwa dashi ba.

Bayanan sun ce David Shikfu Parradang ya je otal din Joy House Hotel dake Area 3 inda ya biya kudin daki na kwana daya dubu 22. Ya shiga otal dinne da misalin karfe 12 na yamma da bakar mota kirar Mercedes Benz.

Jim kadan bayan shigarsa sai ya baiwa me karbar baki dake aiki a otal din umarnin ta shigo masa sa wata bakuwa da yayi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda 'yansanda suka bi sahun farar hula suka tsere yayin da bata gari suka sace akwatin zabe a wata mazaba dake jihar Ondo

Da misalin karfe 4 na yamma bakuwar ta fita ta tafi abinta.

Da Misalin karfe 4 na dare sai ga abokinsa soja yana nemansa, ko da suka shiga dakin sai suka tarar dashi a zaune kan kujera ba rai.

Sun yi gaggawar sanar da ofishin ‘yansanda dake Durumi inda aka je aka dauki gawarsa zuwa Asibiti dan bincike.

hukumar ‘yansandan tace har yanzu tana bincike kan lamarin inda tace a guji yada jita-jita musamman ta garkuwa da mutane dan gudun kawo rudani cikin mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *