
Hukumar ‘yansandan farin kaya, DSS ta bukaci kafar sada zumunta ta X wadda aka fi sani da Twitter data goge shafin mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.
Hukumar ta wallafa bukatar hakanne a shafinta na X din inda take zargin Sowore da yada labaran karya da kuma kawo barazanar tsaro saboda wallafa cewa shugaba Tinubu yace ya magance matsalar rashawa da cin hanci a Najeriya amma kuma ba haka bane.
DSS sun ce sun baiwa kafar ta X awanni 24 su goge shafin na Sowore ko kuma su dauki matakin da ya dace akan kafar.
DSS sun ce wannan ikirari na Sowore ya jawo har zanga-zanga an yi wanda hakan yake barazana ga zaman lafiya a Najeriya.
Dan haka sukace Sowore da kafar data bashi dama ya wallafa irin wannan labari na iya fuskantar hukunci.