
Wata hukumar tsaro a jihar Anambra ta bayyana aniyarta na fara kamen mata dake shigar banza wanda ke yawo babu rigar nono ko dan kamfai a cikin mutane.
An nadi sautin sanarwar inda aka rika yayatashi a kafafen sadarwa.
Hukumar tsaron ta bayyana cewa, Gwamnan jihar, Chukwuma Soludo ne ya bayar da umarnin yin hakan, saidai gwamnatin jihar bata fitar da sanarwa ba game da lamarin.
Sanarwar tace mata masu saka dan kamfai kadai suma za’a fara kamasu.