Tuesday, October 13
Shadow

Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 36 wajan Tafiye-Tafiye a shekarar 2024

Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta a kashe Naira Biliyan 36.3 wajan tafiye-Tafiye a shekarar 2024 data gabata.

Kafar Open Treasury Portal ce ta bayyana hakan a wasu bayanai data tattara inda tace shugaban ya kashe kudadenne wajan tafiye-Tafiye zuwa kasashen waje.

Bayanan sunce idan aka hada da kudaden da shugaban kasar ya kashe a tafiye-Tafiyen da yayi na cikin gida, ya kashe jimullar Naira Biliyan 83 kenan.

Yawan kudaden da shugaban ke kashewa wajan tafiye-Tafiyen sun sakawa ‘yan Najeriya damuwa musamman ma lura da yanda gwamnati ke kukan karancin kudin gudanar da ayyuka.

Peter Obi a kwanakin baya yayi kira ga shugaba Tinubu da ya rage yawan tafiye-Tafiyen da yake yi.

Karanta Wannan  Duk da doka ta bukaci hakan, Ma'aikatan Gwamnatin ciki hadda shugaban kasa, Tinubu, Kashim, da Akpabio sun ki bayyana kadarorin da suka mallaka, kuma an kasa hukuntasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *