
Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayar da shawarar cewa, Muddin Jam’iyyar ADC na son kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 sai Atiku ya rage son rai ya zama mataimakin Peter Obi.
Kungiyar ta bayyana hakane a ranar Litinin a wata sanarwa da shugaban matasa na Kungiyar, Igboayaka O. Igboayaka ya fitar.
Yace Peter Obi na da dukkan abinda ake bukata da zasu kai kasarnan ga ci gaba.