
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, idan jam’iyyar ADC ta bashi takarar shugaban kasa a zaben 2027 tabbas zai kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu
Ya bayyana hakane a kafarsa ta X.
Zan canja kundin tsarin mulki, zan kawo ƙarshen cin hanci cikin wata idan na zama shugaban ƙasa – Amaechi
Tsohon Ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ya jaddada cewa zai canja kundin tsarin mulkin Najeriya idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Amaechi ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a shafin sa na X a ranar Juma’a, inda yace zai kawo karshen matsalar cin hanci a cikin wata daya ko ya sauka daga mulki.
Amaechi ya kuma bayyana Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin lalataccen shugaban hukumar zaɓe a tarihin Najeriya.
Daga Usman Salisu