
Dangin Mafarautan da aka kashe a jihar Edo sun dauki Alwashin daukar fansa muddin ba’a musu Adalci ba.
Mafarautan sun taso daga jihar Rivers ne zuwa garin Kano dan yin bikin Sallah inda aka taresu a Goodwill Junction dake garin Uromi na jihar Edo aka musu kisan gilla da kona gawarwakinsu.
Mafi yawan mafarautan sun fitone daga garin Toranke na karamar hukumar Bunkure a jihar Kano.
Daya daga cikin shuwagabannin kauyen me suna Alhaji Musa Dogo ya bayyana cewa, suna kira ga gwamnati data dauki matakan adalci game da lamarin.
Yace idan ba’a musu Adalci ba, zasu dauki doka a hannunsu.
Hakanan shima wani me suna Bala Danburan ya bayyana cewa sun san duk yanda zasu yi su kutsa kai cikin garin Uromi su daukarwa kansu Fansa.
Mafarautan sun kuma nemi a mayar da shari’ar wadanda ake zargi da aikata wannan kisa garin Kano dan tabbatar da Adalci.