
Lauya kuma dan Gwagwarmaya Bulama Bukarti ya bayyana cewa idan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da gaske yake kan maganar janyewa manyan mutane ‘yansandan dake basu Kariya to ya fara da janyewa dansa, Seyi Tinubu.
Ya bayyana hakanne a matsayin karin haske kan maganar da farfesa, Wole Soyinka yi akan sojojin dake baiwa da shugaban kasar kariya inda yace sun yi yawa.
Bukarti yace maganar farfesa Wole Soyinka maganace akan gyaran tsarin tsaro da ya lalace inda yayi kira ga Gwamnatin Tinubu kada ta ji haushin maganar.