
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, idan ya zama shugaban kasa, zai magance matsalar rashawa da cin hanci a cikin wata daya.
Yace amma ida ya kasa, zai sauka daga shugabancin.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a X.
Ya kara da cewa, kuma zai canja kundin tsarin mulkin Najeriya.
Sannan yace yasan ta inda zai wa Tinubu illa ya ci zabe idan aka zabeshi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC