Monday, December 16
Shadow

IKON ALLAH: Ta Asusun Ajiyar Banki (Account) Aka Tura Milyoyin Kudin Fansarsa

Daga Adam Elduniya Shinkafi

Yau Asabar 05/10/2024 Allah Ya yi wa yayana Mukhtar Elduniya Shinkafi kuɓuta daga hannun ƴan bindiga bayan ya shafe sama da wata ɗaya a hannunsu.

Mun biya maƙuddan kuɗaɗe na fansar sa, bayan shekaranjiya sun bamu account number mun tura masu maira miliyan biyu advance jiya kuma mun kai masu cikon miliyoyinsu.

Muna godiya kwarai da gaske ga ƴan uwa da abokan arziki da suka taimake mu da gudunmawar kuɗi da kuma addu’a da masu ba mu shawarwari muna godiya kwarai da gaske ga kowa da kowa.

Muna addu’a Allah Ya tsare gaba, Ya tsare mu, Ya baiwa Mukhtar lafiya, Ya kuɓutar da sauran bayin Allah da suke hannunsu, Ya maida mana da alkairi akan abubuwan da muka yi asara, mun karɓi wannan ƙaddara/jarrabawa hannu bibbiyu, mun yarda cewa daga gare ka ne.

Karanta Wannan  Kamfanonin Discos sun karawa Mitar wutar Lantarki kudi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *