Friday, December 5
Shadow

In ka ga dama ka tara duka Gwamnonin Najeriya a APC idan ‘yan Najeriya suka ki zabenka dole ka sauka>>El-Rufai ga Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mayar da martani kan yanda Gwamnoni ke rububin komawa jam’iyyar APC.

El-Rufai yace idan gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ga dama, ta tara duka ‘yan Adawa a jam’iyyar APC idan ‘yan Najeriya suka ki zabensa dole ya sauka.

El-Rufai yace kuma hadakar da suke ta ‘yan Adawa tsaf cikin sauki zasu iya kawar da gwamnatin Tinubu ba tare da Gwamna ko daya ba.

El-Rufai ya bayyana hakane yayin ganawa da ‘yan Jarida a Kano, ranar litinin inda yace Idan Tinubu ya ga dama ya tara duka Gwamnonin Najeriya a APC amma idan ‘yan Najeriya suka ki zabarsa shikenan ta kare.

Karanta Wannan  Yaudarar mu ADC suke, ba zasu iya tsinana komai ba ko da sun samu mulki>>Inji Datti Baba Ahmad

A jiyane dai APC ta karbi gwamnan jihar Delta daya canja sheka daga PDP.

Hakanan Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace akwai karin gwamnoni da zasu koma jam’iyyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *