Tuesday, November 18
Shadow

Gwamnoni da yawa zasu dawo APC Saboda Tinubu na mulki na Adalci>>Inji Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da tabbacin cewa, Gwamnoni da yawa zasu sake komawa jam’iyyar.

Ya bayyana hakane a wajan taron karbar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da ya koma jam’iyyar ta APC.

Ganduje ya jinjinawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda shugabanci na gari da yake samarwa a Najeriya.

Ganduje yace a yanzu suna da gwamnoni 22 kenan a jam’iyyar APC inda yace mutane su saka ido su gani akwai karin gwamnonin da zasu dawo APC nan gaba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda matar aure ke lakadawa mijinta duka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *