
Me son kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa, Sunday Igboho ya bayyana farin cikinsa da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
Yace cikin dare Buhari a zamanin mulkinsa ya aika jami’an tsaro su kasheshi, yace amma Allah bai yadda ba.
Yace to yau gashi Buhari ya mutu, Dan haka yana cikin farin ciki.
Lamari dai wasu sun amince dashi inda wasu suka ce bai kamata ba.